Na kasa shiga
Me ke faruwa idan ka gwada?
- Manhajar tana cewa “An samu matsala” idan na shiga ko na yi rajista Sabunta manhajar, sannan ka sake gwadawa da intanet ɗin waya maimakon Wi-Fi na kamfani. Idan har yanzu bai yi ba, gwada app.yumuuv.com a burauza.
- Na taɓa amfani da YuMuuv. Zan sake yin rajista ne ko in shiga? Ka shiga. Taɓa Shiga ka yi amfani da imel ɗinka da kalmar sirrinka; idan ka sake taɓa Yi rajista, za ka ƙirƙiri wani asusu na biyu.
- Manhajar ta ce an kashe asusuna Yawanci mai shirya gasar ne ya dakatar da asusun na ɗan lokaci ko ya kashe shi, misali bayan wata gasa da ta gabata. Ka roƙe shi ya sake kunna shi.
- Ina da asusun YuMuuv guda biyu, ko kuma an jera sunana sau biyu Tuntuɓi sashen taimako ka gaya mana asusun da za mu bari. Za mu goge ɗayan, kuma bayanan ƙalubalen da suka gabata a cikinsa za su ɓace.